Za mu sanya Abuja ta fi ƙarfin ku – Wike ga Ƴan ta’adda
Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Ezenwo Nyesom Wike, a jiya ya fara ziyarar karfafa gwiwa a kananan hukumomin yankin, inda ya bayyana cewa, daga yanzu hukumomin tsaro za su mayar da martani ga ‘yan fashi da makami da ɓarayin daji.
Ziyarar tasa ta zo ne a daidai lokacin da ake yin garkuwa da mutane da kuma kashe-kashen da ‘yan bindiga ke yi a yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN:NUJ ta yi Allah wadai da ƙawanyar ƴan sanda a wani gidan talabijin
Wike, wanda ya ziyarci garin Bwari, hedkwatar majalisar karamar hukumar Bwari, ya gudanar da taron jama’ar gari, sarakunan gargajiya, jami’an tsaro a yankin da sauran masu ruwa da tsaki.
Ana sa ran ministan zai kuma ziyarci wasu kansiloli nan da kwanaki masu zuwa.
A wurin taron, Wike ya bayyana cewa ya isa kuma masu ba da kwarama tawa ɓarayi ba za su ƙara iya kwana lafiya a tsakanin mutanen kirki ba.
Ya ce: “Tsaro na daya daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatin Shugaban kasa ta bada fifiko, shiyasa ya kira wani babban taron tsaro, wanda ya hada da dukkan hafsoshin tsaro, da ministan tsaro, da kaina saboda hare-haren baya-bayan nan, musamman a Bwari ya yi yawa.
“Don haka, a halin yanzu, yana daya daga cikin muhimman abubuwan da ajandar sabunta bege na Mr. Shugaban kasa zai so ya fuskanta.
“Ba zai zama kasuwanci kamar yadda aka saba ba. Zuwana yau shine in nuna muku da gaske muke.
A wani labarin kuma:Wata Sabuwa: Albashin ku na watan Janairu nawa ne – Wani Fasto ga mabiyan sa
Wani limamin cocin Najeriya Fasto Anosike ya shaidawa mabiya cocinsa cewa albashin watan Janairu na shi ne ba na coci ba.
Faston ya yi ikirarin cewa ba ya tsoron koma baya da caccaka, yana mai jaddada cewa abin da suke samu na farko na wannan shekarar nasa ne kawai.