Gwamnatin jihar Edo ta amince da bude makarantun jihar, domin fara sabon zangwana karatu na shekarar 2021/2022 a yau Litinin 6 ga watan Satumban shekarar 2021.
A cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ilimi ta jihar Mrs Stella Maris Imasuen ta fitar, ta ce, Iyaye su tabbatar sun tanadar wa da kayayyakin karatu ga yayan sun, domin fara sabon zangwana karatu.
Ta kara da cewa, ” Muna sanar da al’uma baki daya cewa, musammanma Shuwagabannin makarantun Furamari da na sakandare, na makarantun Gwamnati da masu zaman kansu dake fadin jihar Edo, za a koma makarantu a ranar Litinin 6 ga watan Satumban shekarar 2021, domin fara zangon karatu farko a jadawalin karatun shekara 2021/2022.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Alkalai zasu amsa tambayoyi a gaban Alkalin Alkalai a yau
A cewar ta dukakanin Shuwagabannin makarantun su karbi jadawalin Zangon karatun na farko, na shekarar 2021/2022 wurin jami’in kula da Ilimi na kananan hukumomin su.
“Domin tabbatar da tsaftace cikin makaranta, Shuwagabannin makarantun, su tabbatar an bi ka’idojin hana kamu wa da cutar Corona, Wanda suka hadar da Wajabta sanya takunkumin, amfani da na’uran duba zafin jiki, wanke hannu akai-akai, da kuma amfani da sinadarin wanke hannu wato Sanitizer” inji ta.
A wani labarin Kuma na daban.
Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA da ta kwarar ta ta Nahiyar Africa wato CAF, sun amince da dage wasa tsakanin Guinea da Kasar Morocco da aka tsara buga wa a yau Litinin, a wasan neman gurbin zuwa gasar cin Kofin duniya na shekarar 2022.
Sun yanke hukuncin dage wasan ne sakamakon juyin Mulki da rundunar sojin Kasar da ke yammacin Africa kuma Mai masaukin baki su kayi a jiya Lahadi, tare da tsare Shugaban kasar Alpha Conde.
A cikin wata sanarwa da tagwayen hukumomin su ka fitar, sun nuna cewa, “Yanayin siyasa da kuma tsaron kasar Guinea na Tangal-Tangal, Wanda hukumomin suka lura da hakan,j wajan dage wasan.”
“Domin tabbatar da kiyaye lafiya da tsaron Yan wasa da kuma jami’an wasan daga hukumar FIFA da na CAF, mun amince mu dake wasan neman gurbin zuwa gasar cin Kofin duniya na shekarar 2022 tsakanin Guinea da Marocco.” Inji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa,” Kafin dage wasan an tsara buga shine a Conakry babban birnin kasar Guinea a yau Litinin”
A karshe hukumomin na FIFA da CAF sun ce, da yuwuwar su bayyana bayanan sanya wani lokaci, da za’a buga wasan a yammacin yau Litinin.
Comments 1