.
Alkalin Alkalan Kasar nan Justice Tanko Muhammad a yau Litinin, zai tuhumi Manyan masu shari’a guda shida na jihohi daban-daban, bisa yanke hukunce hukuncen dake cin karo da juna..
Masu shari’an da za su gurfanar gaban Alkalin Alkalan sun hada da na jihar Rivers, Kebbi, Cross River, Anambra, Jigawa da kuma na jihar Imo.
Manyan jami’an Majalisar Shari’a ta kasa a jiya Lahadin, sun tabbatar da cewa,Alkalin Alkalan ya nemi bayanan shari’ar a cikin dukkan kararrakin da aka shigar, Wanda da daga baya aka fara samun sabani.
KARANTA WANNAN LABARIN: Juyin Mulki: FIFA da CAF sun dage wasa tsakanin Guinea da Morocco
Justice Tanko ya kuma gayyaci babban alkalin jihar Delta, kan hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis din da ta gabata, na cire shugaban kwamitin riko na jam’iyar APC Mai Mulki, kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni.
Kazalika akwai yuwuwar Alkalin Alkalan ya zauna taro, tare da Shuwagabannin kungiyar Lauyoyi na Kasa a wannan makon.