Wata kotun koli a garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa ta yankewa wani mutumi mai shekaru 39 a duniya hukuncin kisa, bayan ta kama shi da hannu dumu-dumu da laifin satar mutane, da kuma laifin kisan kai.
Kotun ta kama Datti Buba, mazaunin karamar hukumar Giade dake jihar Bauchi, da laifin satar mutane da kuma kashe mutane biyu daga cikin wadanda ya sata din.
Kotun ta kama Datti da laifuka kala uku, haddin baki wurin aikata laifi, garkuwa da mutane da kuma kisan kai, inji Legit
Alkalin kotun mai shari’a Ubale Ahmed, ya yankewa Mista Buba hukuncin kisa ta hanyar rataye, bisa laifin kashe mutane biyu da ya yi wadanda ya sata a jihar Jigawa.
Wanda ake tuhumar ya shaidawa kotu cewa shi da wasu mutane biyu, Adamu Sabo da Usman Idris, duka daga jihar Bauchi, suka aikata laifin.
Kodayake, kotun ta amince da mutane biyun da Mista Buba ya lissafo, game da laifukan na su. Da yake yanke hukunci akan mai laifin, alkalin ya ce laifin ya sabawa sashi na 97,221 da kuma sashi na 273 na dokar kasa.
Bayan haka kuma kotun ta yankewa Mista Buba hukuncin shekara biyar a gidan yari bisa laifin ta’addanci, da kuma hukuncin shekara 10 bisa laifin garkuwa da mutane.