Hukumar kula da hakkin kwastomomi ta tarayya ta ce za ta cire duk wata manhajar bada lamuni
Da ke cin zarafin kwastomomi sannan ta nemi Google da ya goge irin wadannan manhajoji na dindindin daga kantin sayar da manhajojinsa
Hakan ya kasance a matsayin martani ga ci gaba da cin zarafi da batanci da wadannan masu ba da lamuni na zamani ke yi wa ‘yan Najeriya
Haka kuma shi ne sabon matakin da Gwamnatin Tarayya ta aiwatar don kare yan Najeriya daga ayyukan wadannan masu ba da lamuni na zamani
KARANTA NANYadda Talauci Ya Tsananta A Cikin Kwanaki 40 Na Gwamnatin Tinubu – Hadimin Atiku
A farkon shekarar, FCCPC ta ba da izinin aikace-aikacen lamuni don yin rajista da shi, Ya zuwa yanzu, manhajoji 180 sun samu cikakkiyar amincewa daga hukumar don yin aiki a kasar
A watan Afrilu, Google ya ba da sanarwar cewa manhajojin bada lamuni akan Play Store za su rasa ikon saka lambobin masu amfani ko hotuna daga Mayu 31, 2023
Duk da wannan,manhajojin bada lamuni sun ci gaba da tursasa abokan ciniki saka hotunansu da lambobin BVN
Babban jami’in hukumar ta FCCPC, Babatunde Irukera, ya ce hukumar a shirye take ta rufe ayyukan wadannan manhajoji na dindindin,ya gaya wa jaridar PUNCH
Sakamakon wannan mun fada musu cewa,idan wani daga cikin wadannan sakonni na batanci ko cin zarafi ya sake fitowa, za a cire su, kuma za mu nemi Google ya sauke su na har abada
Ya bayyana cewa yawancin apps da ke addabar kwastomomin suna da sunaye kamar na masu rijista,ya kuma lura yawancin korafe-korafen da muka samu game da waɗannan abubuwa sun nuna cewa kamfanonin ba sa cikin jerin Google
Su ne wadanda ke amfani da WhatsApp, APK, da sauran tashoshi masu laushi,wadanda ba zamu iya game daga ina suke ba
Irukera ya shawarci masu amfani da su da su karɓi lamuni kawai daga manhajojin lamunin da aka amince dasu domin saukin kamowa tare da gurfanar wa idan suka saba doka
A WANI LABARIN KUMA
Tinubu Ya Nuna Cewar Yan Najeriya Basu Yi Asarar Zaben Muslim Muslim Ba-El Rufai
Tsohon Gwamnan Jahar Kaduna Malam Nasir El Rufai ya bayyana cewa yan Najeriya a halin yanzu ba su yi asarar zaben tikitin takarar musulmi da musulmi ba