A dai-dai lokacinda shirye-shiryen zabukan Kananan Hukumomi da Kansiloli a Jihar Katsina,Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta shirya tsaf domin gudanar da gwajin Shan Kwayoyi ga Yan Takararda suka shiga zaben.
Kwamandan Hukumar NDLEA a Jihar Katsina Muhammad Ibrahim ne ya tabbatar da hakan a lokacinda ya karbi bakuncin Kwamitinda Gwamnatin Jiha ta kafa akan yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi gami da kauranci a Jihar.
Mai ba Gwamna Masari Shawara Akan Harkokin Tsaro Alhaji Ibrahim Katsina ne ya jagoranchi sauran mambobin kwamitin a yayin ziyarar da kwamitin ya kai a Hukumomin tsaro dake Jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Ƴan Najeriya na fama da rashin ƙwararru Shuwagabanni masu hangen nesa — IBB
Sauran wurarenda Kwamitin ya ziyarta sun hada da Ofishin Babban Jojin Jihar Katsina,Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar da Rundunar Yansanda da ta Civil Defence gami da Ofishin Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya,wato DSS.
Kamar yadda Kwamandan NDLEA ya bayyana,Hukumarshi tare da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa dake Katsina INEC,sun shirya tsaf domin gudanar da gwajin shaye-shayen ga Yan takarar.
Yace duk dan Takararda aka samu yana shan kwaya,to Hukumar zata shawarci Jam’iyyar shi akan ta sauya shi da wani ko kuma Hukumar NDLEA ta chanza mashi akida.
A nashi bangaren,Babban Jojin Jiha Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar,yace akwai doka da ta yi tanadin ayi gwaji ga duk wani mai neman takara ta kowace kujerar siyasa.
Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar yace,daga halinda ake ciki,duk wanda zai nemi takara a kowane zabe sai Hukuma ta yi mashi gwajin Shaye-shaye domin Kauracewa Shuwagabanni bare gurbi.
A nasu bangaren Sauran Shuwagabannin Hukumominda aka ziyarta,sun bada tabbacin bayar da cikakken goyon baya ga kwamitin domin cimma nasara.
A dukkannin Wurarenda aka ziyarta,Mai ba Gwamna Shawarar akan Harkokin Tsaro Alhaji Ibrahim Katsina,yace ziyarar wani bangare ne na neman goyon bayan masu ruwa da tsaki akan aikinda aka dorawa kwamitin.
Alhaji Ibrahim Katsina ya tabbatar da cewar,Mambobin Kwamitin zasu yi aiki ba sani ba sabo akan duk mai sha ko fataucin kwayoyi gami da kauranci a Jihar.
Daga nan sai ya tabbatar da cewar za’a kafa Kananan Kwamitoci irin wannan a matakin Kananan Hukumomi da Mazabu domin ganin an cimma nasara.
Comments 1