A dai dai Lokacin da Al’ummar jihar kaduna ke dakon Sakamakon Zaben kananan hukumomin jihar da aka gudanar a yau asabar, Sanata Uba sani zababben Sanatan Kaduna ta Tsakiya ya tabbatar da yadda Zaben ya Kasan ce, cikin lumana da kwanciyar Hankali a lokacin da yake tofa albarkacin bakin sa.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da fitar Mai Mai dauke da hotunan yadda ya kada nasa kuri’ar a zaben inda Sanatan ya ce.
“Na shiga cikin sahun sauran masu jefa ƙuri’a a yau, wajen yin amfani da ‘yan cin da demokraɗiyya ta bani, a zaɓukan Ƙananan hukumomin jihar Kaduna.
Sanatan ya kara da cewa, kuma Rahotannin da na samu daga ofisoshin aikina da ke fadin jihar sun nuna cewa, tsarin zaben ya kasan ce cikin kwanciyar hankali da lumana komai ya tafi dai-dai.
“Jami’an hukumar zabe da na tsaro, sun Kasan ce kwararru na musamman, tabbas Ina jinjina da yaba musu sakamakon wannan gagarumar rawar da suka taka, Wannan zaben zai kara zurfafa mahimmancin dimokradiyya a jihar Kaduna, kuma zai kawo ci gaba mai tushe. Inji Sanatan.