Mai shari’a Inyang Edem Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis ya umurci hukumomin tsaro da su bayar da cikakken tsaro ga Murtala Ajaka, dan takarar jam’iyyar (SDP) a zaben gwamnan jihar Kogi da za a yi a watan Nuwamba.
Hukumomin tsaro da abin ya shafa da suka hada da DSS da ’yan sanda, bisa odar, ana bukatar su tabbatar da tsaron lafiyar dan takarar jam’iyyar SDP, har sai an saurari karar da aka shigar gaban kotu.
KARANTA WANNAN: Kotu Ta Dakatar Da Wani Gwamna da Hukumomin Tsaro Daga Kama dan Takarar Jam’iyyar SDP
Umurnin dai ya biyo bayan wata takarda ne da aka shigar gaban kotu a ranar 11 ga watan Yuli, wadda ta nemi a haramtawa jami’an tsaro kamawa, gayyata, tsarewa, ko barazana ga rayuwa da dukiyoyin mai kara har sai an saurari karar da kuma yanke hukunci.
Dan takarar ta jam’iyyar SDP Ajaka ya shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/952/2023 kan gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello; babban sufeton ‘yan sanda da kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi; DSS, da daraktan ta na jihar Kogi; Babban kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC); Babban Hafsan Tsaro, Babban Hafsan Sojoji, da Babban Hafsan Sojan Ruwa a matsayin wadanda ake kara na 1 zuwa 11, bi da bi.
Mai shari’a Ekwo, bayan karanta takardar rantsuwar da Ajaka ya soke don nuna goyon bayansa ga bukatar da kuma abin da lauyansa, S. E. Aruwa, SAN (tare da Divine J. Davies da A. I. Idris) ya gabatar, ya ce bukatar mai nema ta dace kuma a kan haka an ba shi kamar yadda aka yi roko.
“An ba da umarnin hana wadanda ake kara, wakilansu, bayin su, da duk wani wanda ke aiki ta hanyarsu ko a karkashinsu daga kamawa, gayyata, tsarewa, ko barazana ga rayuwa da dukiyoyin mai neman har sai an saurari karar da kuma yanke hukunci.
“An bayar da umarnin tilasta wa wadanda ake kara na 2 zuwa na 11 da su gaggauta bayar da cikakken tsaro ga mai kara a babban birnin tarayya Abuja, jihar Kogi, da sauran wurare a Najeriya har zuwa lokacin da za a saurari karar da kuma yanke hukunci,” inji alkalin.
Kafin ya dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 21 ga watan Yuli, alkalin kotun ya umarci wadanda ake kara dasu yi wa wanda ya shigar da kara hidima tare da duk wani tsari na wannan kara tare da bin umarnin kotu.
A wani labarin kuma, Majalisar Dattijai Ta Amince Wa FG Ta Ciyo Bashin Dala Miliyan $800m daga Bankin Duniya
Yanzu haka dai majalisar dattijai a ranar Alhamis ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na ya ciyo bashin dala miliyan 800 daga bankin duniya.
Hakan ya biyo bayan la’akari da lamunin da Kwamitin ya yi a zaman taron majalisar na ranar Alhamis.