Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Abdul Ningi na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Bauchi ta tsakiya.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Ningi ya samu kuri’u 104,878 inda ya doke babban abokin hamayyarsa Uba Nana na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 84,621.
KARANTA HAKANAN Mahaifiyar Sanata Abdul Ningi Ta Rasu
Jami’in bayyana sakamakon zaben Farfesa Ibrahim Danjuma ne ya bayyana sakamakon a Darazo Collation and Declaration Center a karamar hukumar Darazo a jihar Bauchi.
Haka kuma, Sanata Isah Hamma na jam’iyyar (NNPP) wanda ya zo na uku a zaben ya samu kuri’u 17,995. Kamar yadda jaridar Solacebace ta rawaito
A Wani Labarin Kuma Kabiru Gaya Yaci Taliyar Karshe, Ya Yin Da Kawu Sumaila Ya Lashe Kujerar Sanata
Dan takarar jam’iyyar NNPP mai wakiltar mazabar Kano ta kudu, Abdurrahman Kawu Sumaila, ya doke Sanata mai ci Kabiru Gaya na jam’iyyar All Progressives Congress APC, Daily Trust ta rawaito.
Sumaila, wanda tsohon mai taimaka wa shugaba Buhari ne a majalisar dokoki, kuma tsohon dan majalisar wakilai, ya doke Gaya, wanda ya shafe tsawon shekaru 16 yana mulki.