Mahaifiyar tsohon Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, Abdul Ningi, Hajiya Abu, ta rasu ranar Lahadi a garin Ningi bayan ta yi fama da rashin lafiya.
Daruruwan jama’a daga ciki da wajen jihar Bauchi, ciki har da Gwamna Bala Mohammed, Sarkin Ningi, da manyan ‘yan siyasa ne suka halarci sallar jana’izar da aka yi a fadar mai martaba Sarkin Ningi Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya.
Da yake jajantawa Sanatan, Gwamna Mohammed wanda ya jagoranci manyan jami’an gwamnati zuwa harabar gidan, ya bayyana marigayiyar a matsayin wata ginshiki da ta yi rayuwa mai armashi, ya yi addu’ar Allah ya jikanta da Jannatul Firdaus, ya kuma baiwa ‘yan uwa kwarin guiwar jure wannan rashi.
Da yake mayar da martani a madadin iyalan, Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa ya gode wa gwamnan bisa wannan ziyara da kuma kalaman karfafa gwiwa.