A ranar Litinin Wasu Fusatattun mata sun yi zanga-zanga tsira-tsirara a harabar ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja kan sakamakon zaben shugaban kasa na 2023. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Matan wadanda mambobi ne na kungiyar Free Nigeria Movement, sun kasance a ofishin jakadancin Amurka ne domin gabatar da rahoton magudin da ake zargin an tafka a zaben 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mahaifin Obasanjo Ba Cikakken Bayerabe Bane, Watakila Dan Kabilar Igbo Ne – Fani-Kayode
Masu zanga-zangar wadanda ke dauke da alluna daban-daban, sun yi kira ga gwamnatin Amurka da ta hana wa masu tayar da kayar baya a lokacin zaben biza.
Idan ba amanta ba, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress, APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
An ayyana Tinubu ne a matsayin wanda ya lashe zaben a daidai lokacin da ake zargin an tafka magudi a zabe da kuma a wurare daban-daban a kasar nan.
Tuni dai ‘yan takaran irin na jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na jam’iyyar Labour suka shigar da kara kotun sauraren kararrakin zabe, inda suka nemi a yi musu adalci.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: INEC Ta Sanya Ranar Gudanar Da Zabukan Cike Gurbi
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanya ranar gudanar da zaben cike gurbi na Yan Majalissun tarayya, na jiha da kuma Gwamnoni a wasu jihohin.
INEC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin a shafinta na Facebook.