Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Honorabul Ndudi Elumelu, ya ce ‘yan Najeriya na goyon bayan jam’iyyar PDP muddin idan aka yi zabin da ya dace a babban zaben 2023 da za a yi domin bude sabon shafin Nijeriya na shugabanci.
Elumelu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja a taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na Jam’iyyar PDP na 93.
Ya ce kudurin PDP a taron ta na karshe na NEC da aka gudanar a ranar 28 ga watan Agusta, ta yi ne domin tsara hanyar shawo kan kalubalenta tare da kawo wa ‘yan Najeriya sauki da mafita.
Ya ce a yanzu ‘yan Nijeriya na da yakinin cewa jam’iyyar ita ce kadai hanyar da za ta iya ceto al’ummar kasar a wannan mawuyacin lokaci.
Elumelu ya ce ‘yan Najeriya suna cikin kosawa su ga PDP ta dawo kan mulki don kawo karshen kashe -kashe, ta’addanci, fashi, matsalar tattalin arziki, talauci da rashin fata.
Ya kuma nemi membobin majalisar wakilai ta kasa na PDP da su goyi bayan jam’iyyar yayin da take tattaunawa kan kwace mulkin Nijeriya a 2023 daga taronta na ranar 30 ga watan Oktoba da za a gudanar.