Akalla mutane 65 ne Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa EFCC ta kama a ranar Asabar, 18 ga watan Maris, 2023, a fadin jihohi 28 da aka gudanar da zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha bisa zargin sayen kuri’u, Punch ta rawaito.
20 daga cikin wadanda ake zargin jami’an hukumar na shiyyar Ilorin ne suka kama su yayin da suka kama wasu mutane 13 da ake zargin suna aikin sa ido kan zabe a shiyyar Kaduna.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Gwamna: Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa, Adamu Ya Yi Rashin Nasara A Akwatin Zabensa
Jami’an tsaron da suke sa ido a zaben a shiyyar Fatakwal sun kama mutane 12 bisa laifuka daban-daban da suka hada da jawo masu kada kuri’a don zaben ‘yan takarar da suke so, yayin da rundunar shiyyar Uyo ta kama mutum hudu a Calabar. Sauran wadanda ake zargin an kama su ne a jihohin Gombe, Sokoto, Kebbi da Neja.
Shugaban hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a wata sanarwa da wakilinmu ya samu.
Ya kara da cewa wadanda aka kama a Kaduna sun kunshi maza 10 da mata 3, inda ya ce jami’an da ke aikin leken asiri ne suka kama su.
Uwujaren ya ce, “Wani wanda ake zargi da hannu wajen siyan kuri’u an kama shi ne a hanyar makaranta, Unguwan Rimi Kaduna. Wanda ake zargin wanda da farko ya ki amincewa da kama shi, yana nan a tsare, har sai an kammala bincike.
“Haka nan a Kaduna, tawagar jami’an tsaron karkashin jagorancin Esmond Garba sun kama Buhari Muhammed a rumfar zabe mai lamba 002 dake Dogara Yaro Dagari. An kama shi ne da takardun shaida na masu kada kuri’a, wadanda ya ce za a yi amfani da su wajen ganowa da biyan wadanda suka zabi jam’iyyarsa.
“Bugu da kari, tawagar da ke sa ido kan zaben da aka gudanar a kusa da LEA Kabala Doki, Kaduna karkashin jagorancin CSE Wakilu Omokide ta kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi da sayan kuri’u. Bayan kama su, an kwato jimillar kudi N67, 500, jerin sunayen masu kada kuri’a da lambobinsu na PVC da bayanan asusun ajiyarsu na banki da dai sauransu.
Mai magana da yawun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ya bayyana cewa, bincike ya zuwa yanzu ya nuna cewa, babban tsarin gudanar da wadanda ake zargin shi ne bayar da kudi, tura kudi ta hanyar taransifa, takardun shaida, da bada katin kiran waya ga wadanda suka cancanci kada kuri’a domin su sa su zabi ‘yan takararsu.
“Binciken da aka yi wa mutane da wayoyinsu ya nuna cewa yawancinsu an tura kudi a asusun wasu masu kada kuri’a a cikin jerin sunayen da aka kwato daga hannunsu. Wasu daga cikin abubuwan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da katunan zabe, kudade, jerin sunayen da ke dauke da sunaye da bayanan asusun masu kada kuri’a. Wasu kuma kudin kiran waya ne,” inji shi.
Hakazalika jami’an rundunar hukumar ta jihar Kaduna ta kama wasu mutane biyu a jihar Neja bisa zargin sayan kuri’u. Wanda ake zargin na farko mai suna Umar Ibrahim, an kama shi ne a sashin zabe na titin Peter Sarki bisa samun bayanan sirri.
“Bayan binciken motarsa, an gano wata alama ta INEC (mai sa ido kan zaben cikin gida) mai dauke da sunansa da hotonsa da kuma wasikar nadi daga BOS (Bago Support Organisation) a matsayin Darakta Liaison. A ci gaba da bincike, ya bayyana cewa wani Mista Usman Mohammed, wanda ke cikin jam’iyyarsa ta siyasa ya ba shi lambar shaidar INEC.
Uwujaren ya kara da cewa, “An kama wanda ake zargin na biyu Isa Salihu Bababida a Unguwar Nassarawa da jerin sunayen da dama da kuma BVN.”
Ya kuma bayyana cewa, a garin Fatakwal na jihar Ribas, tawagar masu sa ido kan zaben sun kama wasu mutane 10 da ake zargi da hannu wajen tada zaune tsaye a hanyar Moscow Road, Elekahia, Township, Mile 2, mazaba ta 2 rumfar zabe ta 2 data 30, Ogbum, Phalga, Port Harcourt. .
Uwujaren ya kuma kara da cewa, mutane 20 da rundunar shiyar Ilorin ta kama su ne Adekunle Ademola, Wasiu Raimi, Laaro Rasheed, Alagbe Taiwo, Boniface Victory, Kayode Toba, Adeoye Adetunji, Lawal Favour, Abidoye Moradeyo, Magaji Iliasu, Abdulkadir Abdulmumini da Musa Ola.
Sauran sun hada da Marudeen Sadiq, Abogunrin Oluwasesan, Funmilayo Lawal, Olawuyi Bolarin, Garuba Ismail, Abiola Abogunrin, Amidu Tiamiyu da Usman Abdulazeez.
A halin da ake ciki, kakakin na EFCC ya kara da cewa, a Gombe, hukumar shiyyar Gombe karkashin jagorancin Faruk Dogondaji, ta kama mutane 10 bisa zarge-zargen da ake yi musu na sayen kuri’u, tare da kwato nadin 43 da tsabar kudi N1,923,900.
Sai dai ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike don gano laifin kowane mutum da ake zargi.
A wani labarin kuma, Zaben 2023: PDP Ta Lallasa APC A Gidan Gwamnatin El-Rufai
Jam’iyyar adawa ta PDP ta doke jam’iyyar APC a daya daga cikin rumfunan zabe da ke gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim, Kaduna a zaben gwamna da aka yi ranar Asabar.
Dan takarar babbar jam’iyyar adawa, Isa Ashiru Kudan, ya lashe rumfar zabe mai lamba 014 da kuri’u 77 yayin da Uba Sani na APC ya samu kuri’u 40.