Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya mika wa ‘yan takarar kananan hukumomi a karkashin jam’iyyar APC 44 tuta a shirye-shiryen zaben kananan hukumomi da za a gudanar a jihar.
Zaben dai zai gudana ne a ranar 16 ga watan Janairun 2021.
An gudanar da taron mika tutar ne a dakin taro dake Sani Abacha Stadium a ranar Alhamis a Kano.
Da yake magana a wurin taron, Gwamna Ganduje ya shawarci masu zabe a jihar da su dangwalawa ‘yan takarar APC domin samun kyakkyawan shugabanci da romon dimokuradiyya. Ya kara da cewa; gwamnatinsa ta gudanar da ayyuka daban-daban wajen bunkasa jihar baki daya.
Gwamnan ya ce zabar ‘yan takarar APC zai kawo ci gaba mai dorewa a jihar. Ganduje ya tabbatar da cewa an yi wa dukkanin ‘yan takarar gwajin kwayoyi da hukumar NDLEA ta yi a jihar.
Shugaban APC na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas, ya roki ‘yan jihar da su zabi APC duba da ayyukan da Ganduje ke shimfidawa a jihar.