Sanata Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP ya lashe kananan hukumomi 17 cikin 30 a zaben gwamnan jihar Osun.
Gwamna mai ci Adegboyega Oyetola na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu nasara a sauran kananan hukumomi 13.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ke tattara sakamakon zaben gwamna da aka gudanar a ranar Asabar.
Aikin tattara kuri’un, wanda aka fara tun da sanyin safiyar Lahadi, yana ci gaba da gudana a ofishin INEC da ke Osogbo, babban birnin jihar.
Ife East LG
APC – 19,353
PDP – 18,071
Ife South LG
APC – 12,481
PDP – 9,116
Atakunmosa East LG
APC – 7,449
PDP – 6,992
Irewole LG
APC – 18,198
PDP – 14,216
Egbedore LG
APC – 9,228
PDP – 13,230
Ede North LG
APC – 9,603
PDP – 23,931
Ejigbo LG
APC – 14,355
PDP – 18,065
Isokan LG
APC – 10,833
PDP – 10,777
Ede South LGA
APC – 5,704
PDP – 19,438
Iwo LGA
APC – 17,421
PDP – 16,914
Ola Oluwa LGA
APC – 9,123
PDP – 7,205
Aiyedaade LG
APC – 14,527
PDP – 13,380
Ori Ade LG
APC – 14,189
PDP – 15,947
Irepodun LG
APC – 12,122
PDP – 14,369
Ife Central LG
APC – 17,880
PDP – 13,532
Ifedayo LG
APC – 5,016
PDP – 4,730
Ife North LG
APC – 9,964
PDP – 10,359
Olorunda LG
APC – 18,709
PDP – 21,350
Orolu LG
APC – 9,928
PDP – 10,282
Obokun LG
APC – 9,727
PDP – 13,575
Boripe LG
APC – 21,205
PDP – 7,595
Odo Otin LG
APC – 13,482
PDP – 14,003
Aiyedire LG
APC – 7,868
PDP – 7,402
Ilesha West LG
APC – 10,777
PDP – 13,769
Ifelodun LG
APC – 16,068
PDP – 17,107
Atakunmosa West LG
APC – 6,601
PDP – 7,750
Ila LG
APC – 11,163
PDP – 13,036
Osogbo LG
APC – 22,952
PDP – 30,401
Ilesha East LG
APC – 13,452
PDP – 10,969
Boluwaduro LG
APC – 5,649
PDP – 5,869
A wani labarin kuma na daban.
PDP na zane APC a Zaɓen Osun – Adeyanju ya bayyana inda za’a iya yin Maguɗi cikin Dare
A yayinda sakamakon zaben Gwamnan Jahar Osun yake cigaba da fitowa inda ake kusan ɗaya, Fitaccen mai ƙare haƙƙin Deji Adeyanju ya bayyana cewa Jam’iyyar PDP tana baiwa Jam’iyyar APC kashi a zaɓen.
Adeyanju ya gargaɗi PDP akan saurin taya murna ko sakon murna.
A wani sako daya fitar, Mai Fafutukar yace dukkanin abinda ya sanya a gaba shine sakamakon zaɓen Ile Ife, saboda ana iya Maguɗin shi a cikin dare
Ya bayyana irin yadda aka yi Maguɗin zaɓe na sakamakon Shekarar 2018.
Ya rubuta “PDP na zane APC a Osun, Amma kowa ya maida hankali ga sakamakon Ile Ife. Kada ku manta da 2018, wanan shine yanda suka canja sakamakon zabe da daddare.”
Sakamakon daga adireshin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC ya nuna cewa PDP ke kan gaba.