Gwamna Agboyega Oyetola na jihar Osun ya roki magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu bayan ya sha kaye a zaben da ya gudana, a hannun Sanata Ademola Ademola na jam’iyyar PDP.
Oyetola ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Mista Ismail Omipidan, ya fitar ranar Lahadi a Osogbo.
Ya ce jam’iyyar APC ta amince da sakamakon zaben gwamna kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar a ranar Lahadin nan.
Gwamnan, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta mayar da martani yadda ya kamata bayan nazarin sakamakon da kuma tuntubar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
Oyetola ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, kuma jama’ar jihar su ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da wata matsala ba.
Gwamnan ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar da bin doka da oda.
Oyetola ya kuma umarci jami’an tsaro da su dauki kwararan matakai domin hana tauye doka da oda.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya rawaito cewa a safiyar Lahadi ne hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka yi ranar Asabar.
Da yake sanar da sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zabe na INEC, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe, wanda shi ne jami’in zaben, ya ce Adeleke ya samu kuri’u 403,371 inda ya doke abokin takararsa, Gwamna Gboyega Oyetola, dan takarar jam’iyyar (APC), wanda ya samu kuri’u 375,027.
NAN ta ruwaito cewa PDP ta yi nasara a kananan hukumomi 17, yayin da APC ta samu nasara a 13.
Kananan hukumomi 13 da APC ta lashe su ne; Ilesa Gabas, Ayedaade, Boripe, Ifedayo, Ife Central, Boripe, Ola-Oluwa, Iwo, Isokan, Irewole, Atakumosa Gabas da Ife Gabas.
Yayin da kananan hukumomi 17 da PDP ta lashe sune; Boluwaduro, Osogbo, Ila, Atakumosa West, Ifelodun, Ilesa West, Odo-Otin, Obokun, Orolu, Olorunda, Ife North, Irepodun, Oriade, Ede South, Ejigbo, Ede North da Egbedore.(NAN)