Sanata Rochas Okorochas ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ba shi da tabbas, yana mai cewa zai iya baiwa kowa mamaki dangane da zabin da ya yi na dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.
Rochas Okorocha, wanda ya taba zama gwamnan jihar Imo sau biyu, yana tsokaci ne kan yakin neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a lokacin da ya bayyana a gidan talabijin na Channels cikin shirin Politics Today a ranar Talata.
Okorocha na daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a yunkurinsu na ganin ya gaji Buhari a 2023.
Tsohon gwamnan ya ce mai yiwuwa ne shugaban kasa yana da wanda ya fi so, amma bai bayyana hakan ba.
Ya kara da cewa zabar wanda zai gaji Buhari zai kasance ne ta hanyar yanayin kasa, muradin jama’a, APC, da dai sauransu.
Okorocha ya ce, “Idan kun san shugaban kasa Muhammadu Buhari, shi janar ne kuma ba a iya hasashensa, Ba za ku iya hasashen abin da zai yi ba.
“Buhari yana da hankali sosai domin yana iya yanke shawarar yin la’akari da wasu abubuwa: zai duba yanayin al’umma ya ga wanda a zahiri zai dace da yanayin al’umma; wanda zai lashe zaben APC domin ko shakka babu baya son rasa kujerarsa zuwa PDP.
Don haka, zai yi wuya a ce wannan mutumin zai iya kuma (mutumin) ba zai iya ba; za a yi shawarwari da yawa.”
Okoracha ya ce jam’iyyar tana duban al’ummar kasar ne ba wai jam’iyyar kadai ba.