Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne masu garkuwa da mutane sun fitar da hotunan wasu da suka yi garkuwa da su a lokacin da suka kai Harin jirgin Ƙasan kaduna a watan jiya.
A cikin hoton farko, wanda da alama an ɗauka da kyamarar Infinix Ai, aƙalla ana iya gano maza 17 cikin mutanen da suka dauka hoton.
A cikin hoto na biyu kuwa, ana iya ganin aƙalla mata 18 tare da yara biyar.
Wannan dai shi ne karo na uku a cikin makonni hudu ‘yan ta’addan za su fitar da hotuna ko bidiyoyin wadanda suka yi garkuwa da su.
Yanzu haka dai wadanda aka yi garkuwa da su sun shafe akalla kwanaki 29 a wani wuri da ba a sani ba, duk da kiraye-kirayen da gwamnati da hukumomin tsaro suka yi na a kwatar musu ‘yancinsu.
Hotunan baya-bayan nan dai na zuwa ne kasa da wata guda bayan da gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa akalla mutane takwas ne suka mutu, wasu 26 kuma suka samu raunuka yayin da aka yi garkuwa da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba a yayin wannan kazamin harin.