Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta kama wasu mutane da ta ce suna da alhakin yin harbe-harbe a wasu sassan jihar a ranar Talatar da ta gabata.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Da yake holan da wadanda ake zargin a shedikwatar ‘yan sanda da ke Abakaliki, babban birnin jihar, kwamishinan ‘yan sandan, Faleye Olaleye, ya bayyana cewa mutanensa sun kama mutane 15 da suka hada da wani mai sayar da ganye da ke shirya wa ‘yan bindigar laya.
An kuma ce wasu daga cikin ‘yan bindigar sun mamaye sassan Abakaliki suna harbe-harbe domin aiwatar da dokar zama a gida da masu fafutukar kafa kasar Biafra suka sanya.
KARANTA WANNAN Yan Sanda Sun Tabbatar Da Janye Dokar Zaman Gida
“An kama mutum 15 daga cikin su har da wani mai magani. Za ka ga allo, kana iya ganin jajayen mayafin da suke sanye shi a ranar, kana iya ganin kayan da su ma mata suka saka.
“Suna shirin sake kai wani hari a yau lokacin da muka kai farmakin muka kama su,” in ji Kwamishinan ‘yan sandan.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa, a ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka tarwatsa ‘yan garin musamman ‘yan kasuwa a kewayen unguwar Ishieke da Ukwuachi na Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.
‘Yan barandan da ke aiwatar da dokar zama a gida da masu fafutukar kafa haramtacciyar kasar Biafra (IPOB) suka sa su, sun haifar da firgici a yankunan yayin da jama’a ke daukar matakan kare kansu.
A Wani Labarin Kuma Yadda JAMB Ta Tabbatar Da Batun Jabun Sakamakon Jarabawar Mmesoma
Dalibar Anambra, Mmesoma Ejikeme a karshe ta amince a gaban wani kwamitin bincike mai zaman kansa da gwamnatin jihar Anambra ta kafa cewa ta yi jabun sakamakon jarabawar da ta yi na shekarar 2023, inji rahoton The PUNCH.
A cikin rahoton da mai magana da yawun hukumar shigar da kara ta hadin gwiwa, Dokta Fabian Benjamin ya rabawa manema labarai a Abuja, kwamitin ya bayyana cewa Mmesoma ba ta bayar da wani dalili na yin jabun ba.
“A cikin jawabin da Ejikeme Joy Mmesoma ta gabatar, a gaban shugaban makarantarta, da kuma sakatariyar ilimi cewa labarin da jami’an JAMB suka bayar gaskiya ne kuma yayi daidai da bayanin abin da ya faru.