Wasu ‘yan bindiga a ranar Talata, sun kai hari a hedikwatar karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, inda suka yi ta harbe-harbe.
Wani mazaunin garin Mustapha Zurmi ya shaidawa DAILY POST cewa galibin mazauna garin sun yi ta guduwa cikin daji domin tsira da rayukansu, yayin da wasu kuma suka kulle gidajensu don gudun kada ‘yan ta’addan su kashe su ko kuma su yi garkuwa da su.
Karanta nanMajalisa Ta Ki Amincewa Da Biliyan 1 Da Aka Ware Don Tafiye Tafiye A Ma’aikatar Zuba Jari
Zurmi ya ci gaba da cewa, jami’an sojin da aka tura garin domin ceto rayuka da dukiyoyin jama’a ba su isa su shawo kan lamarin ba, yana mai nuni da cewa ‘yan bindigar na ci gaba da harbe-harbe tare da tafiya cikin walwala daga wannan yanki na garin zuwa wancan.
Ya kara da cewa babu wanda zai iya tantance adadin mutanen da aka kashe ko aka sace.
Dukkanmu muna tsoron kada ’yan ta’addan sun kashe mu ko kuma su yi garkuwa da mu. Muna fuskantar babban kalubalen tsaro a yankin saboda jami’an soja da aka tura domin yakar ‘yan bindigar ba su isa ba,” inji shi.
Duk kokarin da aka yi na jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abdulahi ya ci tura saboda baya amsa kiran waya.
A wani labarin kumaEFCC Ta Fara Neman Tsohon Minsta A Gwamnatin Obasanjo Ruwa A Jallo
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta bayyana cewa tana neman tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye bisa zargin almundahanar dala biliyan 6.
Agunloye yayi aiki a karkashin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo tsakanin 1999 zuwa 2003.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana hakan ne ta wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ta bukaci duk wanda ya samu labarin inda yake to ya kai rahoto ga hukumar ko kuma ‘yan sanda