Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta bayyana cewa tana neman tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye bisa zargin almundahanar dala biliyan 6.
Agunloye yayi aiki a karkashin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo tsakanin 1999 zuwa 2003.
Karanta nanMajalisa Ta Ki Amincewa Da Biliyan 1 Da Aka Ware Don Tafiye Tafiye A Ma’aikatar Zuba Jari
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana hakan ne ta wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, inda ta bukaci duk wanda ya samu labarin inda yake to ya kai rahoto ga hukumar ko kuma ‘yan sanda.
Sanarwar da EFCC ta fitar na cewa Hukumar EFCC na neman U Agunloye. Kun san inda yake Don Allah kar a yi shakka a sanar da EFCC ko ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
DAILY POST ta tattaro cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gayyaci Agunloye domin amsa tambayoyi kan rawar da ya taka a kwangilar samar da wutar lantarki ta Mambila dala biliyan 6 amma bai amsa gayyatarsu ba.
Yayin da Agunloye ke aiki a karkashin tsohon shugaban kasa, an amince da aikin samar da wutar lantarki na Mambilla amma ana zargin ba tare da amincewar majalisar zartarwa ta tarayya ba.
A wata hira da aka yi da shi, Obasanjo ya jaddada cewa ba shi da masaniya kan wanda ya bayar da kwangilar.
Obasanjo ya kalubalanci Agunloye da ya fadawa ‘yan Najeriya inda ya samu ikon bayar da kwangilar dala biliyan 6 ga Sunrise Power and Transmission Ltd dangane da aikin a 2003.
A wani labarin kumaFarashin Man Fetur Zai Rugurguje Nan Bada Jimawa Ba – Masu Ruwa da Tsaki
A martaninsa, Agunloye ya ce yanayin kwangilar farko na aikin samar da wutar lantarki na Mambilla an bayar da shi ne a matsayin kwangilar ginawa da canja wuri a watan Mayun 2003 karkashin kulawar sa.
Ya ce ba lallai ba ne gwamnati ta biya kobo zuwa Sunrise a karkashin yarjejeniyar ginawa, aiki da canja wuri (BOT) domin sabon kamfani ne da aka yi rajista, wanda aka bayyana kadarorinsa bai kai dala 2,000 ba a lokacin.