Rundunar sojin Nijeriya ta ayyana cewa tana da karfin da za ta iya kawo karshen ta’addancin Boko Haram idan har aka samar musu da kayayyakin aiki wanda zai taimaka musu wajen aikata hakan.
Rundunar sojin ta ce daya daga cikin abin da yake kawo mata cikas wajen kawo karshen Boko Haram a arewa maso gabashin kasarnan, shi ne rashin ingatattun kayayyakin yaki
Wannan bayanin na fitowa ne daga bakin Manjo Janar Olusegun Adeniyi, Kwamandan Atisayen Lafiya Dole, inda ya jaddada cewa; rashin kayayyakin yaki wanda ya hada da jirage yana daga cikin abubuwan da suka hana kawo karshen ta’addanci a Nijeriya.
Manjo Janar Olusegun Adeniyi, ya bayyana hakan ne a yayin da ya karbi bakuncin hadin guiwar Kwamitin majalisa a garin Maiduguri da ke jihar Borno a jiya.