Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Ogun Olaposi Oginni, ya ce a zaben Gwamnan jihar Ogun da za a gudanar, jam’iyyar su zata kafa tarihi wajen kawar da sauran jamiyyu tare da kwace ikon jihar.
Oginni ya bayyana haka yayin wata hira da aka yi da shi, yana mai cewa zasu Yi amfani da gazawar APC ta fuskoki da dama, wajen ganin sun yi nasara a zaben Gwamnan da ake sa ran gabatarwa nan gaba.
KARANTA ANAN: FG Ta Yi Rashin Nasara Kan Karar Data Shigar Na Mika Wani Dan Kasuwa Zuwa Amurka
A cewarsa, jam’iyyar su na daya daga cikin manyan jam’iyyar uku da ake ji da su a Najeriya da kuma jihar, don haka baya tantama cewa zasu Yi Nasara akan sauran jam’iyyun.
Ya kara da cewa jam’iyyarsu ma da tsaruka masu kyau da zasu ciyar da jihar Ogun Gaba, a don yake ganin cewa sune zasu gaji kujerar Dapo Abiodun a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2022.
A wani labarin kuma: Peter Obi Bashi Da Wani bambanci Da Atiku, Tinubu – Dan Takarar ADC Kachikwu
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Dumebi Kachikwu, ya bayyana cewa babu bambanci tsakanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi, dana jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da kuma na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
Kachikwu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s a cikin shirin Politics Today.