Zan Dawo da ƙimar shirin NYSC – Mukaddashin DG
Mukaddashin Darakta Janar na Hukumar Kula da Matasa ta Kasa, Mrs Christy Uba, a ranar Alhamis ta yi alkawarin dawo da martabar hukumar NYSC tare da inganta su.
Ta yi magana ne a Abuja a wajen bukin bude taron hadakar ‘yan jarida da hulda da jama’a, da jami’an yarjejeniya da ‘yancin yada labarai na 2022.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nan bada jimawa ba Kiristocin Arewa zasu bayyana wanda zasu marawa baya — Dogara
“Muna so mu maido da kwarin gwiwar ma’aikata da kuma mutanen Hukumar domin su san cewa babu abin da ya canza a NYSC.
“Har yanzu muna kan tsarin da ya kasance a bayyane na ɗan lokaci yanzu, babu abin da ya canza,” in ji ta.
A wani labarin kuma: Za Mu Yiwa Gwamna Sule ritayar Siyasa a 2023 – PDP
Jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa ta sha alwashin tura gwamna Abdullahi Sule kasar Saudiyya a shekarar 2023.
Mista Francis Orogu, shugaban jam’iyyar PDP na jihar ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai a karamar hukumar Karu a ranar Alhamis.