Daga: Abbas Yakubu Yaura
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce zai jagoranci fitar da Najeriya daga cikin duhu idan aka zabe shi a 2023.
Ya na mai da martani ne kan matakin da ma’aikatan wutar lantarkin suka dauka na masana’antu a ranar Laraba, wanda ya kai ga rufe manyan tashoshin wutar lantarki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kungiyar Dalibai NANS Ta Mayar Da Martani Kan Kalaman Ministan Ilimi Na Maka ASUU A Kotu
Sai dai an dawo da wutar lantarki bayan da ma’aikatan suka amince da dakatar da yajin aikin na tsawon makwanni biyu, tare da biyan bukatar gwamnatin tarayya.
A cikin jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce maganin da ya yi na magance matsalar wutar lantarki a Najeriya ya fi daukar hankali.
Ya yi ikirarin cewa manufarsa na da nufin jawo jarin da ya dace a fannin wutar lantarki.
Abubakar ya ce zai cire samar da wutar lantarki daga cikin jerin kebantattun ya ba jihohi.
“Bayan na lura da ci gaban da ake samu a fannin wutar lantarki a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, na sake gamsuwa da cewa mafita ta kan matsalar wutar lantarki, kamar yadda yake kunshe a cikin daftarin manufofina, ‘alkwarin da na yi da ‘yan Nijeriya, shi ne shirin da ya fi daukar hankali wajen fitar da Najeriya daga cikin duhu.
“A dangane da haka, hanyata ita ce, da farko na cire dukkan sarkar darajar wutar lantarki daga jerin kebantattun da ba jihohi ikon samar da wutar lantarki, watsawa da rarrabawa kansu.
“Rikicin masana’antu da Gwamnatin tarayya a Abuja bai kamata ya shafi masana’antu a Legas ko masana’anta a Aba ko Kano ba ko ma dan Najeriya wanda kawai yake son dawowa gida, kallon labarai da barci a karkashin fanka,” ya rubuta.