Sabon Kwamishinan Yansanda na Jihar Katsina Idris Dauda Dabban, ya gargadi Yan Ta’adda masu tada kayar baya a Jihar akan su shiga hankalinsu domin cikin ikon Allah sai ya ga bayansu.
CP. Dauda ya bayyana hakan ne a lokacinda ya karbi ragamar jagorancin rundunar a yau Juma’a 18 ga watan Fabrairu na wannan shekara da muke ciki.
KARANTA WANNAN LABARIN: CBN ta wayar da kan mutanen Delta akan amfani da kuɗin eNaira
Kamar yadda Kwamishinan ya bayyana, zai tsaya daga inda AIG.Sanusi Buba ya tsaya, wanda shine Dauda din ya gada bayanda ya samu karin girma.
Daga nan sai ya roki al’ummar Jihar Katsina, musamman wadanda suke a yankunan da matsalar tsaro ta shafa akan su baiwa Jami’an Yan Sanda hadin Kai da ya kamata domin a cimma nasara.
Ya kuma hori jami’anshi akan su kara azama akan yadda suke kokari wurin yakar Yan Bindiga domin ganin an kakkabe su daga Jihar baki daya.