Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya yi alkawarin ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen hada kan kasar nan, bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Ya kuma tabbatar da cewa a shirye yake, domin ci gaba da tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin Najeriya da kasar Amurka.
KU KARANTA: Wani Tsohon Gwamna Ya Ki Amsa Gayyatar EFCC, Ya Bada Dalili
Shugaban na Najeriya mai jiran gado ya ba da wannan tabbacin ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho a daren ranar Talata da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.
Tinubu ya ce daga cikin abubuwan da zai sa a gaba shine samar da gyare-gyaren hukumomi da shirye-shiryen ci gaba don zurfafa cibiyoyin dimokuradiyya da kuma kawo taimako ga talakawan Najeriya.
Ya bayyana aniyarsa na karfafa tsarin dimokuradiyyar Najeriya da kuma yiwa jama’a hidima a matsayin shugabansu, a cewar wata sanarwa da kakakinsa Tunde Rahman ya fitar.
A tattaunawar da ta dauki kusan mintuna 20 ana tattaunawa, Tinubu ya yi magana game da balaguron da ya yi a Amurka a shekarun baya, inda ya kammala karatunsa na girmamawa a matsayin akawu a shekarar 1979.
Ya kuma tunatar da yadda Amurka ta ba shi mafaka a lokacin baya, saboda jajircewarsa na fafutukar tabbatar da dimokradiyya a Najeriya, lokacin da gwamnatin mulkin soja ta marigayi Janar Sani Abacha ta tilasta masa gudun hijira.
A yayin da yake tabbatar da dimokradiyyar sa, Tinubu ya bayyana cikakken imaninsa cewa sakamakon zaben da ya yi nasara a fili ya nuna muradin al’ummar Najeriya.
Tsohon gwamnan na Legas ya ce zai yi kokarin hada kan kasar nan tare da tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun ji dadi tare da cin moriyar dimokuradiyya da shugabanci na gari.
Tinubu ya bukaci Amurka da ta samar da muhimmin matsayi na Najeriya a Afirka tare da bayar da taimako a fannin tsaro da zuba jarin tattalin arziki domin al’ummar kasar su jagoranci hanya da kuma zama abin koyi ga sauran kasashen nahiyar.
A nasa jawabin, Sakataren Amirkan Anthony Blinken ya ba da tabbacin cewa ya kamata Najeriya ta yi fatan samun kyakkyawar alaka mai amfani da juna da Amurka.
A wani labarin kuma: Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Tsunduma Yajin Aiki
Kungiyar Likitoci masu Neman kwarewa ta Najeriya ta fara yajin aikin gargadi na kwanaki biyar.
Fara yajin aikin ya biyo bayan gazawar gwamnatin tarayya wajen biyan bukatun kungiyar tsawon lokaci.