Kotun Majistare a Kano a ranar Juma’a ta umurci Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, da ya gudanar da bincike kan Sheikh Abduljabbar Kabara bisa zarginsa da bata suna da kuma barazanar kisa.
Mai Shari’a Mustapha Sa’ad-Datti na kotun majistare din, shi ne ya bayar da umurnin sakamakon korafin da lauyan Sheikh Abdallah Pakistan wato Abdulrahman Nasir ya shigar gaban kotun.
Wadanda ake kara a korafin sune Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara da kwamishinan ‘yan sanda.
Umurnin mai dauke da lamba KA/CMC14/003/2021 ta umurci Kwamishinan ‘yan sandan jihar da ya kamala bincikensa zuwa ga kotun kafin 27 ga watan Maris.