Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya rattaba hannu kan kasafin kudi na shekarar 2021 wanda majalisar dokokin jihar Borno ta amince da shi.
Sai dai an ƙara kasafin daga Naira Biliyan 208, zuwa Biliyan 248 biliyan,da zummar samar da masana’antar sarrafa roba, da kuma katafaren otal na ƙasa da kasa ga jihar.
Yayin da yake sanya hannu kan kasafin a ranar a dakin taro na gidan gwamnati da ke Maiduguri, gwamna Zulum ya umarci dukkan ma’aikatu, da hukumomi da sassan gwamnati da su bi ka’idojin kasafin.
Ya kuma umurci mambobin majalisar zartarwarsa su duƙufa wajen hidimtawa al’ummar jihar wajen samar musu da ayyukan raya ƙasa da aka tanada a cikinsa.
Gwamnan ya bayyana cewa a wannan shekarar, 2021, gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko kan tsaro, da ilimi, da Kiwon lafiya, da noma, da samar da ruwan sha da sake gina wuraren da yan tada ƙayar baya suka lalata.
Good luck