Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin ƙaddamar da shirin ɗaukar mutum 774,000 ɗauki a faɗin ƙasar.
Ƙaramin Ministan Ƙwadago Festus Keyamo ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi.
“Shugaba Muhammadu Buhari ya sahale ƙaddamar da shirin Special Public Works na ɗaukar ‘yan Najeriya marasa aikin yi guda 774,000 aiki,” in ji ministan.
Ya ƙara da cewa “za a fara aikin ne daga gobe Talata, 5 ga Janairun 2020. Duka ofisoshin hukumar ɗaukar aiki (NDE) na jihohi sun shirya tsaf domin fara shirin.”
Gwamnati ta tsara ɗaukar mutum 1,000 aiki daga kowace ƙaramar hukuma 774 na ƙasar domin rage yawan matasa marasa aikin yi a ƙasar.
An sha ce-ce-ku-ce tsakanin Mista Keyamo da ‘yan Majalisar Wakilan Najeriya game da wanda ya kamata ya aiwatar da shirin, inda suke neman a ba su wani kaso na mutanen da za a ɗauka.