By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Babagana Zulum ya ziyarci sojojin da suka samu raunuka a wani kazamin fada da aka gwabza a ranar Juma’a, tsakanin sojoji da ‘yan ta’addar ISWAP a garin Rann dake kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru a yankin Kala Balge dake karamar hukumar Jihar Borno tsakiyar.
Zulum, a daren ranar Litinin, ya zanta da kuma jajanta wa dukkan sojojin da abin ya shafa a asibitin sojoji dake Barikin Maimalari,a Maiduguri.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa gwamnan ya samu tarba daga babban kwamandan runduna ta 7 na rundunar soji, Birgediya Janar Abdulwahab Eyitayo.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin a fitar da kudi Naira miliyan 5 nan take a raba wa duk sojojin da lamarin ya shafa har da wadanda ba su da alaka da yakin Kala-Balge, a cewar sanarwar.
Zulum wanda ya samu rakiyar dan majalisar jiha mai wakiltar Kala Balge da kwamishinonin shari’a da na kananan hukumomi da masarautu, ya jajanta wa sojojin tare da godewa da kuma yaba musu bisa ga kishin kasa da suka nuna.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Brig.-Gen. Onyema Nwachukwu, a cikin wata sanarwa daya rabawa manema labarai, ya bayyana cewa maharan sun tarwatsa manyan motoci da babura tare da kai farmaki kan dakarun da aka girke a sansanin sojoji na Forward Operational Base dake Rann, inda sojojin suka kashe mutane 26 tare da kama motocin yaki na ‘yan ta’addan, bindigu AK 47 guda 18 da kuma bindigu kirar M-21 guda daya dauke da alburusai masu yawa.
Rundunar ta kara da cewa an kuma lalata wasu kayan aiki da dama.inda Sojojin suka tilasta wa ‘yan ta’addan “wasu watsi da aikin nasu, su janye cikin rudani”, duk da cewa “abin takaici, jami’ai biyu da sojoji biyar sun biya mafi tsadar farashi, yayin da jami’ai uku suka samu raunukan harbin bindiga” aka kai su asibiti.