By Abbas Yakubu Yaura
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga dake aiki a kan hanyar Shinkafi-Moriki-Kaura Namoda a jihar Zamfara, sun tare hanyar, inda suka far wa fasinjoji inda kuma suka kashe mutane akalla bakwai tare da kona motoci da kayan abinci da dama.
Wani mazaunin yankin mai suna Musa Shuaibu ya tabbatarwa da jaridar PUNCH cewa ‘yan bindigar sun yi nasarar far wa motoci 15 tare da kona biyar daga cikin motocin.
Shu’aibu yace, “Sun yi awon gaba da fasinjoji da dama daga cikin wadannan motocin, inda suka tafi dasu zuwa inda ba a san inda suke ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Wasu daga cikin motocin da abin ya shafa, a cewarsa, sun hada da motocin Golf guda uku, babbar mota daya mai dauke da tumatur, da kuma wata motar Sharon.
Sannan yaci gaba da cewa ‘yan ta’addan suna kan hanya tun ranar Larabar makon daya gabata, yana mai korafin cewa “sun kona motoci biyar da kayayyaki na miliyoyin Naira tare da lalata motoci da dama”.
Shu’aibu ya kuma bayyana cewa,a yanzu haka hanyar kusan ba kowa, yana mai bayanin cewa, “Ba wanda zai iya wucewa ta wannan hanyar sai dai idan ta zama tilas.
“Da kyar za ka ga masu ababen hawa suna bin hanyar saboda yawan ‘yan bindigar dake karkashin shugabansu Bello Turji.”
Duk kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan ya ci tura, domin ba a samu samun kakakin rundunar ‘yan sandan SP Mohammed Shehu ta wayar tarho ba.