Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da Sakandare, JAMB ta bai wa makarantun gaba da Sakandare damar fitar da gurbin shiga makarantun daga ranar 21 ga watan Agusta.
Hukumar ta bada wannan umurnin ne ta hanyar Kakakinta, Dr Benjamin Fabian, inda ya tabbatar da cewa hukumar ta bada umurnin ne a cikin dokokin da ta fitar na 2020 kan bada damar gurbin shiga makarantun gaba da Sakandare.
Dr Fabian, ya ce a cikin dokokin, hukumar ta yi gargadi akan a yi hattara da amfani da fom fiye da daya, inda ta shawarci masu siyar da fom kan wasu darussa da su yi watsi da hakan.
Ta kuma shawarci makarantu akan su shawarci dalibai akan su nemi darussan da suke so ta hanyar Ofishin hukumar, inda suka ce dukkan gurbin shiga makarantun gaba da Sakandare za a gudanar da shi ne a hukumar.