Nijeriya ta soma yunkurin karbar kudaden da adadinsu ya kai dala biliyan 62 daga wasu manyan kamfanonin hakar mai dake kasar, kudaden da ta ce ya kamata kamfanonin su biya ta a tsawon shekara 20 da suka gabata.
A shekarar 1993, dokar da gwamnatin Nijeriyar ta kafa kan sa ido bisa aikin hakar danyen man da kasafta ribarsa ta fayyace cewar, kamfanonin za su kara adadin kudaden harajin da suka biyan kasar, idan farashin gangar danyen man ya zarta dala 20.
Bayan soma aikin dokar a waccan lokacin, kamfanonin hakar man sun amince da biyan kashi 20 na ribar da suke samu duk shekara ga Nijeriya. Sai dai duk da cewar farashin gangar danyen man ya daga sosai cikin sama da shekara 20 da suka gabata, ba a waiwayi dokar sabunta harajin da ya kamata kamfanonin su rika biyan gwamnatin Nijeriyar ba. Wannan ce ta sa a yanzu, kasar ta ce lokaci ya yi da kamfanonin za su cika tsohuwar yarjejeniyar da ta cimma da su, ta hanyar biyan basukan harajin da basu saka a lalitar ta ba, da adadinsu ya kai dala biliyan 62.
Sai dai da alama manyan kamfanonin hakar man ba su amince da ikirarin gwamnatin Nijeriyar ba, domin kuwa tuni suka daukaka kara kan batun.
Kamfanonin da Nijeriya ke neman hakkin na ta na ribar dala biliyan 62, sun hada da Equinor (Norvège), Esso (Exxon Mobil), CNOOC (China) da kuma Shell.