Babbar Likitan Babban Asibitin Karu Dr Osamuede Ojo ta koka akan yadda matsalolin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ke cigaba da haifar da taɓin hankali a ƙasar.
Dr Osamuede Ojo tana jawabi ne a lokacin bikin bada tallafi kashi na biyu domin gyara ɗakin yara da manya a Babban Asibitin Karu dake Abuja, wanda Lions Club International ta shirya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa ta yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 14 a Indiya
Tace bincike ya nuna cewa, ɗan shekara 7 an shigar dashi cikin waɗanda suke ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, inda tace akwai ƙarancin cibiyoyin mahaukata da ƙwararru a Abuja.
Mataimakin shugaban Ƙungiyar Lions Club Architect Samuel Egbuchiri, tayi kira ga masu hannu da shuni dasu taimaka domin kammala cibiyar.