An kama Isah Barnabas, Mataimakin Sufeto na ‘yan sanda (ASP), wanda ya yi wa wani matafiyi mummunan rauni a Okene na jihar Kogi.
Tun da fari dai, an ruwaito cewa, Jami’an da suka hadar da: Sufeto Ifediegwu Godwin, Sajan Emmanuel Ochima, Kofur Umameh Mathias da Barnabas an ce sun karba cin hanci da rashawa daga daya daga cikin matafiyi da suka gani dauke da kwamfutar tafi -da -gidanka.
Wani matafiyi, wanda ya kalubalanci daya daga cikin jami’an, an mari shi a bainar jama’a.
Faifan Bidiyon lamarin ya tayar da hankular al’uma, inda da dama ke kira ga hukumomi da su ladabtar da jami’an.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa ta yi sanadiyar Mutuwar Mutane 14 a Indiya
A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, William Aya, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, ya ce, an cafke Barnabas.
Aya ya ce, ban da Barnaba, sauran jami’an da ke da hannu a zargin karban kudaden, su ma an cafke su.
Ya Kuma kara da cewa, jami’an ‘yan sandan suna aikine a Ofishin Yan sanda na Adogo ne, da ke jihar Kogi.
“Rundunar‘ yan sandan jihar Kogi ta fara gudanar da bincike kan wani faifan bidiyo da ke nuna yadda jami’an ‘yan sanda da ke aiki a sashen Adogo, yayin da suke aikin sintiri a kan hanyar Adogo zuwa Okene, aka Samu rahoton karban kudi Naira dubu ashirin da biyar (N25,000) daga matafiyi, yayin kuma daya daga cikin mutanen da ke sanye da kakin soji ya yi masa rauni. ” inji sanarwar.
“Kwamishinan‘ yan sandan jihar Kogi, CP Idrisu Dauda Dabban, psc (+), fdc, yayin da yake Allah wadai da lamarin, ya lura cewa, an gano jami’an‘ yan sandan kuma an tsare su a sashin binciken manyan laifuka na jihar.”
“An bai wa Mataimakin Sufeto Janar na‘ yan sanda (ASP) wata tambaya a hukumance, yayin da sauran kananan jami’an uku (3) a halin yanzu ke fuskantar shari’ar daki daki (ayyukan ladabtarwa na cikin gida na ‘yan sanda).”
“Kwamishinan ya ci gaba da cewa, rundunar na yin iya bakin kokarinta don kulla hulda mai da wadanda abin ya shafa. Ya yi kira ga wadanda abun ya shafa da su tuntubi rundunar ‘yan sandan a kan lambar waya kamar haka: 08107899269.” A cewar shi.
“Ya ba da tabbacin cewa duk wani jami’in da aka samu a cikin binciken za a hukunta shi daidai da laifin shi,” in ji sanarwar.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin hana ranar tunawa da zanga -zangar EndSARS da ya fara gudana a shekarar da ta gabata.
Zanga -zangar wacce ta girgiza al’ummar kasar nan a bara, ta kasance zanga -zangar nuna kin jinin cin rafin da rundunar ‘yan sandan Nigeria ke yi wa al’umar kasar.
Sai dai daga bisani zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali a wasu sassan kasar nan.