Ƙarancin Naira Ya Fara Ƙamari A Abuja
Wasu sassan babban birnin tarayya Abuja sun fara fuskantar karancin kudin Naira a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke kara kusantowa a bikin Kirsimeti.
A kalla bankuna guda bakwai a unguwar AYA da ke Abuja sun kasa raba kudi a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN:Hukumar NPC ta Gargadi Jami’anta Game da Magudin Bayanai
Wakilin DAILY POST, wanda ya ziyarci wadannan na’urorin ATM a yammacin ranar Alhamis, ya ruwaito cewa bai iya janyewa ba, kuma kusan mako guda kenan da faruwar lamarin.
Wakilinmu, ya lura cewa, masu sana’ar POS, sun yi layi a kan lambobin su a gaban wadancan bankunan domin yin sana’ar gaggauwa.
Daya daga cikin ma’aikatan POS, wanda ya bayyana kansa a matsayin Samuel, ya koka da yadda na’urorin ATM din ba sa raba kudi kamar yadda ake tsammani.
Ya lura cewa ana samun kuɗi ne kawai a wasu sa’o’i na ranar.
“Tun da muka shiga watan Disamba wadannan na’urorin ATM din ba su da yawa.
“Akwai karanci naira kuma mai yiyuwa ne saboda muna gab da watan Disamba, amma CBN ne kadai zai iya bayyana wannan sabon karancin,” inji shi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Babban Bankin Najeriya CBN ya ba da umarnin cewa duka tsofaffin Naira da aka yi wa gyaran fuska sun ci gaba da zama a kan doka a Najeriya.
Kotun kolin kuma a hukuncin da ta yanke ta amince da buƙatar gwamnatin tarayya da ta dage wa’adin ranar 31 ga watan Disamba kan amfani da kudi N200, N500, da N1,000.
Yayin da yake mayar da martani kan hukuncin, CBN ya ce: “Don kauce wa shakku, Kotun Koli ta ba da umarnin cewa tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da N1000, tare da sake fasalin su, za su ci gaba da zama kan doka.
“A bisa ga sashe na 20 (5) na dokar CBN ta shekarar 2007, duk takardun kudi da babban bankin Najeriya ya fitar za su ci gaba da zama a kan doka har abada.