Misis May Ikokwu, shugabar kungiyar, Save Our Heritage Initiative, wata kungiya mai zaman kanta, a ranar Juma’a ta yi kira da a karfafawa matasa ta hanyar koyon sana’o’i don samar da arziki da kuma kawo karshen rashin tsaro.
Ikokwu ta yi wannan kiran ne a wata tattaunawa da ta yi da Kamfanin dillancin labarai na Kasa Najeriya, NAN, a yayin bikin ranar basirar matasa ta duniya, a Abuja.
Ta bayyana damuwarta kan yawaitar tabarbarewar tsaro, shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran munanan dabi’u a tsakanin matasa, inda ta bayyana cewa karfafar su da isassun sana’o’i ya zama wajibi ga ci gaban kasar nan.
A cewarta, matasa da dama na tabarbarewa sakamakon rashin aikin yi, lamarin da ya janyo yawaitar laifuka kamar satar mutane da kuma fashi da makami.
Ta yi kira ga gwamnati da ta samar da hanyoyin fitar da matasa daga kan tituna ta hanyar gudanar da ayyukansu masu inganci.
“Yawancin matasan da ke yawo a kan tituna suna da baiwa daban-daban da ke jiran a yi amfani da su don amfanin kasa,” inji ta.
Ikokwu ta bukaci gwamnatocin tarayya da na Jihohi da su gaggauta daukar mataki, ba wai kawai don ceto matasa daga aiki ba, sai dai a samar da arziki ta hanyar sana’o’i.
“Matasan a yau sune makomarmu da gadonmu. Ya zama wajibi mu tabbatar da cewa an kama karfin su gaba daya,” in ji ta.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa ta ruwaito cewa, ranar 15 ga watan Yulin kowacce shekara ce ake bikin ranar basirar matasa ta duniya, bayan da majalisar dinkin duniya ta sanar da wanzuwarta a shekarar 2014.
Manufar Ranar Ƙwararrun Matasa ta Duniya ita ce ‘bikin mahimmancin samar wa matasa sana’o’in yi, aiki mai kyau, da kuma kasuwanci’. (NAN)