Kakakin kungiyar dattawan arewancin Najeriya Dakta Hakeem Baba-Ahmad ya cc ya zargi jam’iyyar APC mai mulki a kasar nan da yunkurin wargaza kasar.
Ya ce tabbas a shekara ta 2023 Najeriya za ta kara shiga wani hali idan ba a ɗauki mataki ba, wacce a matsayin ta na uwa mabada mama a nahiyar Afirka bai kamata hakan ya faru ba.
Baba-Ahmad wanda ya bayyana haka a tattaunawrsa da tashar talabijin ta Channels TV yayin wani shirin ta mai suna Politics Today wato siyasar mu a yau, ya ce duk jam’iyyar da za ta gaji APC a 2023 akwai gagarumin aiki a gabanta.
Kasar nan dai ta jima tana fama da yake yaken ta’addanci, al’amarin da ya yi sanadiyar salwantar rayukan Mutane akalla 40, 000 yayin da ya raba dubbanni da matsugunansu.