Wata kotun Appeal dake jamhoriyar Benin, ta sanar da cigaba da tsare mai mafutukar kafa kasar Yarbawa Sunday Igboho har sai ta kammala bincike akan zargin da ake kansa. Jaridar The news Nigeria ta wallafa a shafinta
Jaridar BBC News Yoruba, ta wallafa cewa Kotun ta bada umarnin fitar da Sunday Igboho daga Ofishin Yan sanda na Cotonou, inda yanzu haka yake tsare a gidan kurkuku.
A dai satin daya gabata ne aka tsare Sunday Igboho tare da matarsa akan hanyarsu ta zuwa kasar Jamus.
KARANTA:- NCDC ta ce sabon nau’in cutar korona na Delta ta bulla kasar har mutane 10 sun harbu
An dai cafke shine bisa umarnin da hukumar binciken sirri na Kasar Najeriya ta sanar kan nemansa ruwa a Jallo.
Hukumar ta binciken sirri na Kasar Najeriya, na neman Sunday Igboho ruwa a Jallo ne bisa laifin Jagorantar zanga-zanga a garin Ibadan da kamashi da mallakan manyan Makamai a gidansa inda ya misanta cewar ba nasa bane.
Bayan dai gwamnatin Kasar Cotonou ta kamashi, kasar Najeriya sun bukaci da su damkashi a hannunsu don amsa laifinsa na tada tarzoma da mallakan manyan Makamai.
An dai gurfananar dashi a gaban Kotu a ranar Alhamis kamin a daga karar zuwa ranar Litinin 27 ga watan July.
A wani labarin
An gurfananar da wani matashi a Kaduna kan damfarar miliyan 6.7
Hukumar EFCC reshen Jahar Kaduna tayi nasarar cafke wani matashi mai suna Aliyu Iliyasu bisa laifin cin amana, inda hukumar ta gurfananar dashi a gaban mai Shari’a M. T. Tukur, a wata babban Kotu dake Kaduna.
An fara tuhumarsa kamar haka inda akace ” Kai Aliyu, a watan rana cikin watan Disamba na shekarar 2019, Kotu na tuhumarka akan zunzurutun kudade kimanin miliyan shida da dubu dari bakwai da saba’in da biyar (#6775000.00), inda Abubakar Sarki ya baka domin ka saya masa mota kirar Mercedes Benz GLK SUV, inda kaci amana akan hakan, wanda wannan yayi dai-dai da laifin cikin kundin Shari’a na Kotun Panel na sashi 296 na shekarar 2017, a Kaduna. Wanda hakan nada hukunci a sashi na 297 a kundin Shari’a Kotun Panel.
Amma sai dai bai amince da tuhumarsa da akeyi ba, sai dai alkali mai kare Kotu Jamil Musa, ya roki kotun data sanya rana da za’a fara gudanar da wannan Kara. Sannan shi kuma Alkali mai kare Aliyu Iliyasu ya bukaci kotu data bashi beli.
Mai shari’a Tukur, ya baima Aliyu Iliyasu beli akan naira miliyan daya, tare da gabatar da shaidu kwarara guda uku.
Sai dai matsalar ta dawo sabuwa, inda Abubakar Sarki ya tura karar ga hukumar ta EFCC, inda yace a wata rana cikin watan Disamba na shekarar 2019, ya baiwa Aliyu Iliyasu kudi naira miliyan shida da digo bakwai kan ya saya masa mota, amman sai ya kawo masa wadda ba ita suka shirya ba.
Shidai Abubakar Sarki a lokacin bai karbi motar ba, inda Aliyu Iliyasu