Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasar Ingila sun kafa wani tarihi a tsakiyar makonnan a gasar zakarun nahiyar turai wato a wasanni na biyu na rukuni na sabuwar kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 da aka fara fafatawa a makon daya gabata. Akwai ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa guda 4 da suke wakiltar ƙasar ta Ingila a gasar zakarun nahiyar turai.
A gasar dai akwai Chelsea da Manchester City da Liverpool da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United wanda sune masu waklitar ƙasar ta Ingila.
Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan na Ingila dai sun kafa tarihin buga wasanni dukkaninsu batare da anjefamusu ƙwallo a zare ba, sannan kuma kowacce ta sami nasara a wasan data fafata. Haka zalika sun jefa adadkn ƙwallaye guda 14 a zare wanda kusan wannan shine karon farko da suka kafa irin wannan tarihin.
Ga jerin yadda wasannin suka kasance:
Manchester City sunci 3.
Liverpool sunci 2.
Chelsea sunci 4.
Manchester United sunci 5.
Ana ganin idan Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasar Ingila suka ci gaba da fafata wasa ahaka to zata iya yiwwuwa wata a cikinsu ta lashe gasar ta zakarun nahiyar turai.
Rabon da wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ingila ta lashe gasar zakarun nahiyar turai tun a shekarar 2018 da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta lashe a wasan ƙarshe da suka fafata da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham.