Wasu ‘yan bindiga a safiyar yau Talata sun kai hari a rukunin gidajen ma’aikatan Jami’ar Abuja (UniAbuja) inda suka yi awon gaba da wani Farfesa a fannin tattalin arziki, Obansa Joseph, da ‘ya’yansa biyu, da kuma wasu mazauna unguwar.
Wata majiya kuma mazaunin unguwar da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce ‘yan bindigar sun kai farmaki ne a rukunin manyan ma’aikatan da ke Giri a karamar hukumar Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja da misalin karfe 1:00 na safiyar ranar Talata, inda suka dauki tsawon sa’a guda.
Ba a iya tabbatar da sunayen ‘ya’yan Farfesan biyu da su ma aka sace ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
PREMIUM TIMES ta rawaito cewa sauran wadanda abin ya shafa sun hada da wadanda kawai majiyar ta bayyana sunayensu “Barrister John, Fidelis da Mallam Sambo.”
Kakakin Jami’ar, Habib Yakoob, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce wadanda abin ya shafa kusan shida ne.
“Eh, na tabbatar da cewa bayanin gaskiya ne. Baya ga farfesa da ’ya’yansa, akwai wani ma’aikacin da ba na bangaren koyarwa ba. Kimanin su shida ne aka kashe,” in ji Mista Yakoob.
Sai dai ya kara da cewa an hada jami’an tsaro domin kwato musu ‘yancinsu.
Mista Obansa tsohon dalibi ne a Jami’ar Abuja da Jami’ar Legas, wanda bincikensa ya hada da Kiwon Lafiya da Tattalin Arziki.
Har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, har yanzu ba ta amsa tambayoyin wayar tarho dangane da harin ba.