Ƴan Bindiga Sun Sace Ƴan Uwan Ɗan Takarar Gwamnan APC A Katsina
Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane shida a garin Dutsinma, hedikwatar ƙaramar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina.
An ce wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun kasance ƴan uwan Ɗan Takarar Gwamna ne Umar Tata Tsauri.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa, waɗanda akayi awon gaba dasu sun kasance baƙi ne a wani ɗaurin aure a gidan da ke kusa da gidan fitaccen Ɗan siyasar, wanda ya tsaya takarar neman tikitin tsayawa takarar Gwamna na jam’iyyar APC a Zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da aka yi a kwanakin baya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fusatattun mutane sun kashe wani Ɗan Fashi da Makami da yaƙi Tuba
“Matar da aka yi garkuwa da ƴaƴan Ƙanwar Ɗan siyasar ce (Tata) kuma maharan sun nufi gidan kai tsaye inda suka yi awon gaba da matan, wannan abin tambaya ne matuka,” in ji wata majiya.
Wani mazaunin garin Dutsinma da ya nemi a sakaya sunansa ya ce da farko ‘yan ta’addan sun yi garkuwa da mutane tara a Unguwar Kudu da ke garin, amma daga baya aka sako mutane uku.
“Na farko, sun bar wata tsohuwa wadda ba za ta iya tafiya ba, tare da wani karamin yaro da ke ci gaba da kuka. Sannan suka tafi.
“Akwai lokacin da ‘yan fashin suka zo Dutsinma kwanaki hudu a jere suna garkuwa da mutane. Lamarin ya kara ta’azzara kuma a gaskiya mun damu,” inji majiyar.
Har ila yau, wani basaraken gargajiya da ba ya son a buga sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce “Mun dawo daga gidan da lamarin ya faru, mun jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa.
Ya kara da cewa, “Hakika lamarin (‘yan bindiga) yana ƙara dagulewa kuma muna kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen magance matsalar.”
Kakakin Rundunar Ƴan sandan, SP Gambo, bai iya tabbatar da faruwar lamarin ba har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, domin ya ce har yanzu ba a yi masa bayani ba, amma ya yi alkawarin sanar wa da zaran ya samu bayanan.