Tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a Kano, Alhaji Inuwa Waya, ya bayar da gudummawar ofishin yakin neman zabensa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Ahmad Bola Tinubu, jaridar primetimenews ta rawaito hakan.
Ofishin yakin neman zaben mai dauke da dakunan zama 10,000, an ce dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tunubu ne zai kaddamar da shi da kansa a wasu makwanni masu zuwa.
Karanta kuma: Da Ɗuminsa: APC ta tabbatar da Lalong a matsayin DG na yakin neman zaben Tinubu
Da yake jawabi yayin karbar ofishin yakin neman zaben da ke kusa da titin Zaria mai yawan jama’a, Kodinetan Kano na yakin neman zaben Bola Ahmad Tunubu, Alhaji Baffa Babba DanAgundi, ya ce Waya ya nuna matsayinsa a fagen siyasar jam’iyyarsa.
“Wannan wani Mutum ne (Inuwa Waya) da Gwamna Ganduje ya nemi ya janye burinsa na Gwamna a tsakiyar bukatarsa, inda aka tsayar da dan takarar Mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna kuma ya yi hakan ne ba tare da wata tangarda ba kuma yau maimakon ya manta da kowa yanzu yana bayar da gudummawar ofishin yakin neman zabensa”.
Ya ce a lokacin da ya samu labarin, Dan takarar Shugaban kasa Tunubu ya ce ya gamsu sosai da abin da Inuwa Waya ya yi masa don haka zai zo kaddamar da ofishin da Kansa.
Mallam Inuwa Waya tsohon Daraktan kamfanin mai ne na NNPC mai ritaya ya yi takarar kujerar tsohon birni tare da sauran mutane da dama.
A wani labarin kuma: APC ta shirya don fara yakin neman zabe – Lalong
Jam’iyya Mai mulkin kasa APC ta ce ta kusa fara yakin neman zaben Tinubu/Shettima a matsayin yan takarar shugaban kasa da mataimaki.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Gwamna Simon Lalong ne ya bayayana hakan ga manema Labarai a Abuja.