Ƴan bindiga Sun Saki Matar Kwamishinan Filato, Ɗiyar ta
Matar Kwamishinan Mahalli na Jahar Filato Usman Bamaiyi da Ɗiyar ta, an sace su kwanaki 11 da suka gabata, sun shaƙi Iskar Ƴanci daga hannun wanda suka sace su.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar Usman Bamaiyi, Matar Kwamishinan Mahallin da Ɗiyar ta, an sace su a lokacin da ƴan Ta’adda suka yi ƙawanya a gidan Kwamishinan dake Al’ummar Gindiri, Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jahar a farkon ranar Asabar 9 ga watan Afrilu na Shekarar 2022.
Wata Majiya a Al’ummar Gindiri ta shaidawa Jaridar Daily Post, cewa an sake su zuwa ga Iyalan su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mayakan ISWAP sun kashe wani dan banga dan shekara 17 tare da sace ‘yan mata a Chibok
A cewar Majiyar “mutane biyun da aka sacen sun samu ƴancin kai a daren ranar Litinin.”
Matar Kwamishinan da Ɗiyar ta an sace su a Gindiri, a gidan su a sanyin safiyar Asabar 9 ga watan Afrilu ta Shekarar 2022.