Aƙalla Mutane 109 Rundunar Ƴan Sandan Jahar Gombe ta kama sakamakon shigowa Najeriya ba bisa ƙa’ida ba daga Jamhuriyar Benin.
Waɗanda aka kama sun ƙunshi ƴan Ƙasar Benin 4 da ƴan Najeriya guda 2.
Dayake bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga Manema Labaru, Kwamishinan Ƴan Sandan Jahar Ishola Babaita, ya bayyana cewar an kawo su ne zuwa Jahar a Motoci guda 3 daga Benin, tare da taimakon ƴan Nijar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta bada umarnin a tsare Matar Makashin Hanifa, Jamila
Babaita ya bayyana cewar bayan an tuhume su, sun bayyana cewa su mambobin QNET ne, wani shiri na Kafar Sadarwa ta zamani.
Yace “a ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2022, Rundunar ta samu bayanai cewa akwai wasu motoci guda 3 sun ɗauko mutane guda 109.
A lokacin da yake bayyana rashin jindaɗi na bude sana’o’i marar tushe, Babaita ya bayyana cewa dukkanin wanda ake zargi za’a kaisu Kotu.
“Al’umma zasu so, suji cewa wata tawaga tare da ƴan Najeriya da Ƴan Benin. Sun shigo nan ƙasar ba tare ƙa’ida ba. Daga binciken mu, mun gano cewa mutane sun shiga wata sana’a ne domin su damfari mutane,” inji Babaita.
A jawabin shi, Adolphe ya bayyana cewar daga Benin sun zone domin su wayar wa mutane kai akan ƙudirin su na wayar wa mutanen Gombe akan sana’ar su.
Ya musanta aikata ba dai-dai ba, yace ƙudirin su, shine su wayar wa Al’ummar Gombe kai.
“Mun zo ne Gombe saboda Jasper da Abdullahi ƴan Najeriya, sun gayyato mu akan kasuwancin QNET. Wannan shine karo na farko amma ban taɓa ganin su ba, kafin yanzu,” inji shi.
Shima dayake jawabi, Solomon Micah yace ya shiga kasuwancin da Naira 500,000.
Comments 1