Babban Kotun Majistare ta Jahar Kano dake zaman ta a gidan Murtala ta kama matar mai garkuwa da mutane, kuma wanda ake zargin ya kashe ƴar shekara 5, Jamila Abdulmalik Muhammad Sani.
Jamila an kama ta sakamakon zargin ta da ake yi da ƙin sanar da wadda aka kama.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da duminsa: ECOWAS Ta Dakatar Da Burkina Faso Daga Cikin Kungiyar Bayan Juyin Mulki
Jamila mai shekaru 30, itace matar Abdulmalik Tanko wanda ke fuskanta tuhuma guda 4 da ƙin sanar da wadda aka sace, zagon ƙasa, sa Garkuwa Da Mutane da kisa.
Ana tuhumar akan taimakon mai garkuwa da mutane a gidan ta, har na tsawon kwanaki biyar.
“Ke Jamila Muhammad Sani, Matar Abdulmalik Tanko Muhammad, mai mallakin makarantar Noble Kids Comprehensive dake a Kwanar Dakata a Jahar Kano, a ranar 4 ga watan Disamba na shekarar 2021 da misalin ƙarfe 6:30 mijinki ya kawo Hanifa Abubakar mai shekarau 5, sanye da kayan makaranta, kuma ta shafe kwanaki 5 a gurin mai garkuwa da mutane.
“Kin ɓoye Hanifa, bayan kinsan cewa an sace ta wanda mijin ki yayi, kuma kika ƙi sanar da kowa,”inji bayanan kotu.
A cewar mai shigar da ƙara, wannan babban laifi ne, kuma ya saɓawa sashe na 227 da kundin tsarin masu manyan laifi.
Amma ta musanta tuhumar da ake yi mata, wanda mai shigar da ƙara ya karanta mata.
Mai shigar da ƙara, Barista Lamido Soron-Dinki ya buƙaci Kotu ta ajiye ta a kurkukun ƴan sanda kafin cigaba da shari’ar.
Babban Jojin,. Chief Majistare Muhammad Jibril ya bada umarnin a ajiye ta sashen kula da manyan laifuka, ya kuma ɗage zuwa 2 ga watan Fabrairu na shekarar 2022 domin cigaba da karanto hujjoji.