Rundunar Ƴan Sandan Jahar Kogi ta kama mutane uku da ake zargin suna cikin wata dabar masu garkuwa da mutane, dake addabar motoci akan hanyar Itobe-Anyigba.
Kayayyakin da aka samu a tattare dasu sun ƙumshi bindiga, da bindiga ƙirar Fistin ta gargajiya, da P.O.S, da gatari, da takunkumi fuska, da kwafsar harsashi guda 5 gami da sarƙoƙi.
Masu garkuwa da mutanen da aka kama, sun ce sune sanadiyyar sace-sacen mutane da dama, sun haɗa da Ɗanlami Shu’aibu, da Kabiru Amodu, da Adejoh Tijani dukkanin su ƴan asalin ƙauyen Adumu ta Ƙaramar Hukumar Ofu ta Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bayan Shafe Kwanaki 10 A Hannun ‘Yan Bindiga limamin Cocin Katolika Na Umuahia Ya sake Samun ‘Yanci
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴan Sandan William Ovye Aya ya fitar a ranar Asabar a Lokoja, inda yace waɗanda ake zargin an kama su ne a yankin Ajaokuta.
Mr Aya yace Ɗanlami da Kabiru Amodu an kama su ne a ranar 16 ga watan Oktoba, biyo bayan wani samame na sirri da rundunar takai.
Yace an gudanar da samamen domin magance ayyukan ta’addanci, ta fuskar yawaitar garkuwa da mutane a Itobe da kewayen ta, musamman akan hanyar Itobe-Anyigba.
Mai magana da yawun Rundunar yace suna ƙoƙari domin gano sauran waɗanda suke ta’addancin a tare domin kaisu kotu.