Ƴan Sanda sun ceto wani Mutum da aka sace a ƙauyen Peter Obi
Masu garkuwa da mutane a Agulu ta Ƙaramar Hukumar Anaocha ta Jahar Anambra a ranar Asabar sun sace wani mutum.
Mutumen wanda aka kama a kauyen Nwanchi dake Agulu, ya kasance anan ne garin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour Party Mr Peter Obi.
KARANTA WANNAN LABARIN: NECO tayi kira da Ɗalibai dasu Jefar da Jita-jitar ɗage Jarabawa, tace za’a fara 27 ga Yuni
An gano cewa, sun sanya mutumen ne a cikin motar sa, ƙirar Lexus 350 Salon, Amma daga baya Ƴan sanda sun ceto da suka bi kadin lamarin.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar DSP Tochukwu Ikenga yace “Jami’an Ƴan Sanda da misalin ƙarfe 4 na yamma, na ranar 25 ga watan Yuni na Shekarar 2022 sun ceto mutumen da aka sace a cikin mota ƙirar Lexus 350 Salon da lambar mota mai rajista EPE 326 HE da wata mota ƙirar Ford SUV da lamba GGD 769 FT akan hanyar Ezinifite ta Ƙaramar Hukumar Aguata.
“An sace shi a sanyin safiyar yau a Kauyen Nwanchi, Agulu. Wanda suka sace shi sun sanya shi a cikin bayan motar.
“Bayan ƴan Sanda sun samu wannan bayanan, sun kara baza ƙaimi. Wannan ne ya sanya bata garin suka sake shi, da motar shi, da tasu motar, suka ruga”.
Ikenga yace biyo bayan ceto shi, wanda ba’a ambata sunan sa ba, Ƴan Sanda sun cigaba da bincike.