‘Rundunar Yan Sanda a Jahar Katsina ta hallaka Yan Bindiga Uku Da Cafke wasu guda biyu tare da Dabbobi
Daga Wakilinmu na Jahar Katsina Usman Salisu Gurbin Mikiya
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a daren jiya Lahadi tayi nasarar hallaka yan bindiga guda 3 har lahira a kauyen Marabar Gurbin Mikiya dake cikin karamar hukumar Kankara.
Haka Zalika, Rundunar tayi nasarar cafke wasu yan bindiga guda biyu da suka kashe wani dan kasuwa Alhaji Ibrahim Kwatahi da ke kauyen Jargaba a cikin karamar hukumar Bakori ta Jihar.
Mai Magana da yawun Rundunar yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya bayyana Haka ga Manema labarai a helkwatar rundunar da ke Katsina a madadin Kwamishinan Yansandan CP Sanusi Buba.
Gambo Isa ya bayyana cewa kashe Yan ta’addan ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu cewa yan bindiga za su biyo ta wani burtali da shanun da suka sato, inda nan take suka hallaka ukku daga cikin su, sauran sun tsere daji da halbin bindiga a cikin daji.
A cikin binciken da Rundunar tayi ta samu bindiga kirar Ak49 guda daya tare da shanu guda dari da sittin da tumaki dari da saba’in da mashina guda biyu a hannun su.
SP Gambo Isa ya kara da cewa daga cikin wanda Rundunar ta cafke akwai Buhari Yusuf dan shekara 25 da Usman Alhaji Bammi Dan Shekara 30 dan asalin Unguwar Mai Kawo ta cikin karamar hukumar Kafur ta jihar, wadanda sune suka kashe Ibrahim Fatahi.
Daga cikin nasarori da Rundunar ta samu sun hada da kama wani Shahararren mai safarar alburasai, Ibrahim Ma’aruf wanda aka fi sani da Risku dan shekara 40 da haihuwa dake kauyen Tashar Bokiti a gundumar Runka ta karamar hukumar Safana a jihar Katsina.
An dai kama shi tsakanin hanyar Dutsinma zuwa Safana dauke da shanun sata arba’in da alburasai 96 na bindigar kirar Ak47 da zunzurutun kudi har naira dubu dari bakwai da tamanin.